Babu wata shawara da ta rage wa Buhari Illa ya fito takara a 2019 – Ahmed Lawan

1

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Ahmed Lawan ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari bashi da wata zabi yanzu illa yayi shirin fitowa takara a 2019.

Lawan ya fadi haka ne bayan ganawa ta musamman da ya yi da Buhari a gidan gwamnati na Aso Rock.

” Duk abubuwan da Buhari yayi alkawarin yi bayan zama shugaban kasa ya cika su, kamar samar da tsaro da zaman lafiya,  bunkasa tattalin arzikin Kasa, da yaki da cin hanci da rashawa.”

Lawan ya ce a dalilin haka duk masoya da magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari na bayan sa kuma suna kira gare shi da ya shirya fitowa takara a 2019.

Sanata Abu Ibrahim wanda shine shugaban gamayyar kungiyoyin da suka zama ‘Buhari Support Organisation’ ya ce sun ziyarci shugaban kasa ne don su sanar dashi ayyukan da kungiyar take yi da kuma abin da ta sa a gaba zuwa yanzu.

Share.

game da Author