Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa ya koka kan halin da wasu asibitocin gwamnatin jihar ke ciki inda ya kara da cewa kamata ya yi a gyara asibitocin yadda mutanen za su sami ingantaciyar kiwon lafiya.
Ya fadi haka ne a lokacin da ya kai wa asibitin dake Umunede ziyaran banzata.
Yayin da yake jinjinawa ma’aikatan kiwon lafiyan asibitin Ifeanyi Okowa ya tabbatar da cewa gwamnatin sa zata gyara asibitocin domin mutane su sami ingantaciyar kiwon lafiya.
Ya ce cikin gyaran da za a yi ya hada da raba dakin yara biyu domin bai kamata yara kanana da manyan yara su dunga kwanciya daki daya ba.
Discussion about this post