APC bata cancanci zama Jam’iyya a kasarnan ba yanzu – Buba Galadima

0

Injiniya Buba Galadima yayi kira ga hukuar Zabe da ta soke rijistan da tayi wa jam’iyyar APC cewa ta karya wasu sharuddan da ya kamata ta cika tun bayan kafa jam’iyyar.

Buba Galadima yace “Sam APC bata cancanci ci gaba da zama jam’iyya a Kasarnan ba saboda ta kara tsarin da y ace dole sai kwamitin gudanarwa da amintattun da sauran bangarori na jam’iyyar da ya hada da kwamitin wakilan tsara manufofin jam’iyyar na Kasa sun gudanar da taro duk bayan watanni uku, Inda har yanzu batayi hakan ba.”

“ Ina daga cikin mutane tara da suka sa hannu a shirya manufofin jam’iyyar APc and kaico, har yanzu abin da muka saw a hannu ba a kai ga aiwatar da ko da daya bane. Sannan jam’iyyar ba ta taba neman mu wadanda suka kafa ta ba domin neman shawara ko kuma yi mana bayani akan nasarorin da aka samu a jam’iyyar zuwa yanzu.”

“ Ban yarda cewa wai jam’iyyar APC ta rataya a wuyan mutum daya bane kamar yadda wasu ke ganin shine karfin jam’iyyar. Jam’iyyar ta kowa da kowa ce.”

Ya ce Buhari bashi da sha’awar yin siyasar jam’iyya, saboda haka bai san ko a wata jam’iyya bane zai yi takaran idan harya ce zai fito takara a 2019.

Share.

game da Author