An zabi Farfesa Joy Eyisi a matsayin mace Mataimakiyar Shugaba ta farko a tarihin Budaddiyar Jami’ar Nijeriya, wato NOUN, jami’ar da ake karatu daga gida.
Hakan ya biyo bayan zaben da aka yi ne ranar Laraba, wanda Majalisar Dattawan jami’ar ne su ka shirya zaben.
Eyisi ta cike gurbin da Farfesa Patrick Eya ya bari tun bayan kammala wa’adin sa. Shi ne zai kama aiki nan da sati daya a matsayin daraktan shiyya mai kula da horaswa kan gudanar da ilmi na budaddiyar jami’a.
Kafin zaben ta Mataimakiyar Shugaban Jami’a mai kula da harkokin ilmi, Eyisi ita ce daraktar ayyuka na musamman a Majalisar Tarayya.
Ta kasance farfesa a fannin Turanci, kuma ‘yar asalin Adazi-Ani, cikin karamar hukumar Ani-Ocha, a Jihar Anambra.
Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Abdalla Uba Adamu na daga cikin wadanda su ka halarci kama-aikin Eyisi, inda ta karba daga Eya. Adamu ya sake nanata yakinin da ya ke da shi cewa matan da ke aiki a jami’ar na daya daga cikin mafi hazikan mata a kasar nan.
Ya kuma jaddada cewa zaben da aka yi wa farfesar ya kara tabbatar da cewa NOUN ba ta bar kowane yanki ko shiyyar kasar nan a matsayin saniyar-ware ba.