An kashe mana yara 6, an waske da shanu sama da 200 a Filato – Miyetti Allah

0

Shugaban kungiyar makiyaya na Miyetti Allah MACBAN reshen jihar Filato Nura Abdullahi ya zargi mazauna karamar hukumar Bassa da aikata kisan gilla kan ‘yan uwansu guda shida ranar Lahadi.

Ya fadi haka lokacin da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da shi ta wayar taraho ranar Laraba inda ya kara da cewa sun sanar wa gidajen jaridu a jihar kan abubuwan da ke faruwa.

Ya kuma ce sun sanar wa jami’an tsaron (‘yan sanda da sojojin ‘Operation safe heven’) da ke karamar hukumar Bassa kan abin da akayi wa ‘yan uwansu a kauyen.

“‘Yan ta’addan Irigwe ne suka far ma wasu makiyaya shida yayin da suke kiwo, suka kama su suka kashe, daga nan kuma suka waske da shanun su.

” A takaice dai iyalen wadannan makiyaya 6 da aka kashe sun yi hasaran dabobi 232.”

Bayan haka shugaban kungiyar matasan Irigwe dake karamar hukumar Bassa Sunday Abdu ya mai da wa MIYETTI in da ya ce ” Na yi bakin ciki matuka yadda Nura abokina ya zargi mutane na da aikata wannan kisa ga ‘yan uwwan su.”

” Babu kiyyaya Tsakani na da Nura amma ina so duniya ta sani cewa Fulani da muka basu wuri suka zauna tare da mu a kwanakin baya sune a yau suke kashe mu tun a cikin watan da ya gabata batare da wani dalilai ba.”

Share.

game da Author