An kama wasu matsafa da sassan mutane, wai su Malamai ne

0

Jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar Ogun sun kama wasu bokaye da ke kiran kansu malamai a wani gida da sassan jikkunan mutane, jini, da guraye na tsafi.

Mutanen masu suna Adebayo Mudashiru (36), Raheed Abass (33) da Rasaq Adenekan (42) sun ce suna wannan sana’a ne don taimakawa mutane masu neman dafa’i da samun Sa’a a rayuwa.

Bayan haka kuma SARS a jihar sun kama wasu barayin da suka shahara wajen Satan katin ATM din mutane.

Share.

game da Author