Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na jihar Adamawa NULGE ta shiga yajin aiki domin nuna fushin su kan rashin biyan ma’aikatan kananan hukumomin albashin da alawus har na watanni biyar.
Kungiyar ta koka da yadda gwamnatin jihar ta maida su ‘yan maula saboda wahalar da ma’aikatan suka shiga sanadiyyar kin biyan su albashi.
A lokacin da yake hira da manema labarai shugaban kungiyar Hamman Gatugel ya ce suna bin gwamnatin jihar bashin albashin watani 5 zuwa 7.
” Mun yi kokarin kai kukan mu ga gwamnatin jihar amma ta yi kunen uwar shegu da mu domin har wani jami’in gwamnati yana yi mana izgili cewa mu je mu ci gaba da yajin aikin.
Hamman Gatugel ya ce saboda hakan ne kungiyar su ta yanke shawaran shiga yajin aiki daga ranar Litini 23 ga watan Oktoba.
Kwamishinan yada labarai na jihar Ahmed Sajoh ya karyata masu yajin aikin cewa ba watanni 5 bane suke bi bashi, wata biyu ne kawai.
Ya ce gwamantin jihar na iya kokarin ta wajen ganin ta biya ma’aikatan albashin su na watanni biyu da suke bin ta.
Discussion about this post