Akwai yiwuwar fama da ambaliyar ruwa da akayi ne ya jawo cutar ‘Monkey Pox’ – Bassey

0

Jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya Bassey Bassey ya ce da yiwuwa cewa cutar ‘Monkey Pox’ na da nasaba da ambaliyan ruwan da kasar nan ta yi fama da shi wannan shekara.

Ya fadi haka ne a taron da kungiyar masana kimiya na Najeriya ta shirya a Abuja.

Bassey ya ce kamar yadda aka sani ne cewa ambaliyar ruwa na da nasaba da yada cututtuka saboda irin abubuwan da ya ke yakan yawo da su kamar kashin dabbobi, rubabben gawawwankin dabbobi da makaman tan su.

“Idan mutane su ka yi amfani da irin wannan gurbatacen ruwan dole ne su kamu da cututtuka.”

Bayan haka shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce akwai yiwuwar hakan kamar yadda Bassey Bassey ya fadi.

Ya ce sanadiyyar ambaliyar ruwan da kasan ta yi fama da shi hukumar su ta wayar da mutanen kasan kan hanyoyin da za su bi domin samun kariya daga kamuwa da cututtuka irin haka.

Share.

game da Author