Uwargidan shugaban Kasa Aisha Buhari ta yi tir da matsalolin rashin kudi da asibitin da ke fadar shugaban kasa ke kukan tana fama da shi.
Ta ce abin kunya ne irin kukan da asibitin ta ke yi na rashin kayan aiki wanda hatta maganin ciwon kai ‘Panadol’ wai babu a asibitin bayan naira biliyan 3 da gwamanti ta ware wa asibitin.
Aisha Buhari ta fadi haka ne a taron da aka yi na masu ruwa da tsaki a fadar shugaban kasa dake Abuja ranar Litini akan haihuwa,Kiwon lafiyar mata da yara kanana RMNCAH+N.
Ta ce ta ji labarin halin da asibitin ke ciki ne wani lokaci da bata da lafiya.
”Na yi mamaki matuka lokacin da aka bani shawaran in ziyarci wani asibiti da bam saboda rashin magani da kayan aiki a asibitin fadar shugaban kasar.”
‘‘Dalilin haka ya sa dole na tafi kasar Britaniya domin samun kula.”
Ta ce a yanzu haka idan ka ziyarci asibitin fadan shugaban kasa zaka ga ana ta gine gine amma kuma asibitin ba ta da kayan aiki ko da sirinjin allura ne.
Aisha ta kara da cewa idan hakan ya same ta a Abuja wani irin hali ne sauran matan gwamnonin jihohin kasar nan ke ciki.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata hukumar asibitin ta nemi izinin mai da asibitin hannun ‘yan kasuwa saboda karancin kudi da take fama da shi a asibitin.
Discussion about this post