Abin da muka yi a fannin tsaro tunda muka hau gwamnati – Buhari

0

TSARO

A fannin tsaro, dole ‘yan Najeriya su yi shukura da jinjina ga zaratan sojojin Najeriya masu jajircewa wajen shigewa gaba su na fatattakar Boko Haram. A yanzu sun kai Boko Haram makurar kakkabe su, sun boye sai dai su rika kai harin sari-ka-noke kawai a daidaikun wurare.

Najeriya na godiya ga kasashe makwauta da kuma kungiyoyin kasa da kasa wadanda su ka taimaka wajen ganin mun cimma kudirin mu na kakkabe burbushin Boko Haram.

Wannan matsalar ta’addanci ta addabi hatta manyan kasashen Turai da wasu yankuna masu ingantaccen tsarin ‘yan sanda, su ma sai da ta’addanci ya zame musu karfen-kafa.

Ba mu bar sojojin mu baya ba wajen inganta ayyukan su, ta habbaka OPERATION LAFIYA DOLE, mun kuma kafa dakarun kai farmakin gaggawa a Arewa maso Gabas. Wannan ne zai kawo yunkurin da mu ke yi na karshen ganin bayan Boko Haram.

Gwamnati na kan kokarin ganin an sako sauran daliban Chibok da ma sauran wadanda ke tsare a Hannun Boko Haram.

Sojoji da sauran jami’an tsaro na bakin kokarin su wajen ganin sun magance matsalar garkuwa da mutane, fashi da makami, rikicin Fulani da manona da sauransu domin kara jaddada tsaro a fadin kasar nan.

Share.

game da Author