A yi hattara da zuwa asibitocin kasashen waje don suna sace sassan jikin marasa lafiya – Inji Ministan Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga ‘yan Najeriya da suke fita kasar waje domin zuwa asibiti da su bi a hankali domin yanzu fa wasu likitoci sace sassan jikin mutane su ke yi.

“Hakin mu ne mu sanar wa mutane abin da ke faruwa a wasu asibitocin waje.”

Isaac Adewole ya yi kira ga kungiyar likitocin Najeriya NMA da su mai da hankali wajen ganowa da dakile irn wadannan ayyuka da wasu likitoci a asibitoci ke yi ganin cewa an kama wasu a kasar masar da suka aikata irin haka ga wasu marasa lafiya su 41.

Ya ce gwamnatin kasar Masar ta lisafo asibotoci 4 da ke aikata hakan a Giza wanda ya hada da Dar al-shefa in Helwan, Cairo; Al-Bashar Specialist Hospital in Faisal, Giza; Al-Amal Centre for General Surgery in Maurinteya, Giza da asibitin Dar Ibn Al-Nafis, Giza.

Haka nan kuma kasashen Malaysia, India da Sin ba a bar su a baya ba wajen aikata irin haka.

Share.

game da Author