Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta maida tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina a cikin gwamnati bayan fallasa harkallar miliyoyin kudi da suka bace a zamanin da yake shugaban hukumar fansho na kasa.
Majiya da dama sun shaida wa Premium Times cewa duk da har yau EFCC na neman Maina ruwa a jallo, amma an wayi gari an maida shi cikin gwamnati a asirce, tare ma da yi masa karin girma zuwa darakta a ma’aikatar cikin harkokin cikin gida.
A baya, Maina shi ne Mataimakin Darakta a wannan Ma’aikatar.
Labarin maida Maina a cikin gwamnati ya fito ne sakamakon wani sakon taya murna da wata kungiya da ake kira League of Society Organization ta yi, inda ta ke jinjina wa gwamnatin tarayya dangane da mayar da Maina a cikin gwamnati.
Idan ba a manta ba, an kori Maina a cikin 2013. Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ce ta kore shi, sakamakon wata takardar da Shugaban Ma’aikata na lokacin ya rubuta ya na neman a kore shi, a bisa zargin harkallar biliyoyin kudaden fansho.
Wani darakta a ma’aikatar ya ce bai kamata a dawo da Maina ba, saboda ya na da tuhumar da ake masa a kotu, wadda ya tsallake ya gudu ya bar kasar tun 2013.
“Kuma doka ta haramta a maido da shi har sai kotu ta wanke shi tukunna.”
Cikin 2012 ne dai aka zargi Maina da yin harkalla har ta naira bilyan 100. A cikin 2010 ne gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada shi ya tsarkake harkar biyan kudin fansho.
Daga zargin da aka yi masa ne Majalisar Dattawa ta gayyace shi. Daga nan ta umarci a gagauta kama shi. Shi kuma Maina sai ya maka Majalisar Dattawa kotu, tare da Sufeto Janar na ‘Yan sanda na lokacin MD Abubakar, kuma ya shiga wasan buya.
An kai karar su a kotu a ranar 21 Ga Yuli, 2015 tare da Stephen Oronsaye. An caje su da aikata laifuka na harkalla har 24. Sauran sun bayyana a kotu, amma shi Maina ya tsere.
An ce Maina ya shafe shekaru a Dubai, inda daga can ya rika kamun-kafa a cikin gwamnatin Buhari domin a maida shi kan mukamin sa.
Babu inda aka bada sanarwar dawo da Maina kan aiki. Abin ne dai gwamnatin tarayya ta yi a cikin sirri.
Dama kuma a farkon wannan shekarar, an rika buga fastar Maina inda ake nuna ya na neman takarar Gwamnan Borno, amma dai ba a ce ga jam’iyyar da ya ke ciki ba.
ZARGIN DAMBAZAZZAU DA MALAMI
Majiya ta ce Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazzau da Ministan Shari’a Abubakar Malami ne su ka shiga su ka fita har aka dawo da Maina a cikin gwamnati.
An ce ya rika tura masu zuwa su na yi masa kamun-kafa tun a lokacin shi ya na Dubai. Premium Times ta nemi taking daga Minista Dambazzau domin jin ta bakin sa, amma bai dauki waya ba.
Kakakin yada labaran Ministan shari’a ya shaida wa Premium Times cewa bai san da batun har an dawo da Maina a cikin gwamnati ba.
EFCC TA YI MAMAKIN DAWO DA MAINA
Wani babban jami’in EFCC ya ce sun yi mamaki matuka da aka dawo da Maina, domin har yanzu hukumar su na neman sa ruwa a jallo. Domin sun gurfanar da shi a kotu, amma ya gudu ya bar kasar.
Daga nan ya ce hukumar su za ta sake bude fayil din sa domin su sake kama shi, tunda a wurin su har yau, su na neman sa.
An tuntubi kakakin yada labaran Shugaba Buhari, amma Femi Adesina ya ce bai san an maida Maina a cikin gwamnati ba.