A BAJE A FAIFAI: Nazarin Ikirari 10 Da Buhari Ya Yi a Jawabin Ranar Tunawa da Samun ’Yanci

0

Ranar Tunawa da samun ’yancin kasa, wacce aka shafe shekaru 57 ana bikin murnar zagayowar ranar, ta kasance wani dandali da gwamnati kan yi jawabai na hadin kan kasa, su bayyana ci gaban da su ka samar da kuma yin jawaban abin da za su samar wa al’umma a shekaru masu zuwa.

Sau da yawa wadannan jawabai kan fuskanci kalubale, musamman inda aka fahimci akwai dungu ko karkataccen zance, ko kuma inda masu nazari ke ganin kamar an nemi a yi wa ’yan kasa ‘yar-burum-burum.

Irin haka ta faru ga jawabin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yayin jawabin sa cikin 2005 da kuma Goodluck Jonathan a cikin 2012, inda ya ce nasarar yaki da cin hanci ta gwamnatin sa ce.

A jawabin da Shugaba Muhammadu Buhari ranar 1 Ga Oktoba, 2017, ya nemi ya yi gurmaden ikirarin aiwatar da wasu ayyuka ko tsare-tsaren da wasu ke ganin kamar akwai bukatar a tantace barcin makaho.

Kan haka ne PREMIUM TIMES HAUSA ta lalubo jawabin, inda ta fede shi dalla-dalla.

A jawabin Buhari, ya ce jam’iyyu ba su fara fara samun nasarar zabe a kananan hukumomi, jiha da tarayya ba, har sai lokacin mulkin sa. Wannan kuwa magana ba haka ta ke ba.

Ya kuma ce a lokacin sa hasken lartarki ya karu a cikin watan Satumba, fiye da zamanin kowane shugaba.

TSINKAYE NA 1:

Shugaban Kasa ya ce: Duk da an rika saida gangar danyen man fetur har dala 100, ana kuma hako har ganga milyan 2.1 a kowane rana kafin hawan sa mulki, an wayi an wawure kudaden, kuma babu kayan more rayuwar al’umma a cikin kasar nan.

“Sannan kuma aka bar mu babu ko taro a asusun gwamnati ba.’’

Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar da cewa a daidai lokacin da Buhari ya hau mulki cikin 2015, akwi har sama da naira bilyan 200 a cikin Asusun Jarin Nijeriya wanda aka kafa cikin 2011. Sannan akwai kuma wasu kudi har dala 2.1 da gwamnatin Buhari ta gada daga ribar gas da ake tattara wa jihohi.

Sannan kuma a lokacin da Buhari ya hau, akwai wata dala bilyan 2. 7 ta rarar cinikin danyen man fetur.

Yanzu kuma sai a sake bincike, shin da gaske ne akwai lokacin da aka rika sayar da gangar danyen man fetur har dala 100 kuma ana hako ganga milyan 2.1 a kowace rana tsakanin 1999 zuwa 2015?

Yayin da bincike da bayanan da PREMIUM TIMES ta samu daga hannun gwamnatin tarayya su ka nuna an dai saida gangar mai dala 61.o7, binciken ya kuma nuna cewa an rika hako har ganga milyan 2.3 a cikin wadancan shekaru.

TSINKAYE NA 2:

Buhari ya ce: “Kafin gwamnatin mu, bakon abu ne jam’iyya mai mulki ta fadi zaben gwamna, zaben Majalisar Tarayya ko na Majalisar Jihohi.’’

Wannan ikirari ba gaskiya ba ne. A zaben 2003 PDP ce rike da gwamnatin tarayya da kuma yawancin jihohi, saboda ita ce ta lashe zaben 1999.

A zaben 2007, jihohi 12 sun fada hannun jam’iyyun adawa, ciki kuwa har da ANPP, jam’iyyar Buhari a lokacin.

A zaben 2011 kuma jam’iyyun adawa sun kara cin jihohi, daga 12 a zaben 2007 zuwa 13 a 2011.

Adams Oshiomhole ya lashe zaben gwamnan Edo ranar 14 Ga Yuli, 2012, har ma ya fito ya gode wa Jonathan saboda abin da ya kira tsame hannun sa daga shiga cikin ruguguwar zabe.

Sai dai kuma a karkashin gwamnatin Buhari, gwamnan adawa daya ne ma ya taba yin nasara. An yi zabukan gwamnonin Bayelsa, Edo da Ondo, inda Edo da Ondo duk APC ce ta yi nasara, yayin da Bayelsa ce kadai jam’iyyar adawa, PDP ta lashe.

TSINKAYE NA 3:

Buhari ya ce sai a yi godiya ga sojjin kasar nan, saboda kakkabe Boko Haram da su ka yi, kuma su ka murkushe su, tare da yin galaba a kan su.

Ko a jabwabin san a 2016 ya bayyana haka. Amma a yanayin yadda ake gani, bai yiwuwa a ce an an gama da Boko Haram, domin har yau sun a kai hare-hare, kuma sojoji na ci gaba da yaki da su.

Ko kungiyar Afuwa ta Duniya ta ce daga watan Afrilu zuwa Satumba, Boko Haram sun kashe mutane 231 a Nijeriya.

TSINKAYE NA 4:

Buhari ya ce cikin Satumba 2017 karfin hasken lantarki ya karu zuwa migawat 7,001

To wannan ba haka abin ya ke ba, domin tun a cikin Janairu zuwa Agusta, 2015 ne hasken lantarki ya kai migawat 7,141.

TSINKAYE NA 5:

Buhari ya ce ya na murnar shaida wa ‘yan Nijeriya cewa yanzu an fara aikin hasken lantarki na Mambila, wanda shekara-da-sheakaru aka gagara a ciki gaba da
Wannan magana akwai gyara. Shi dai wannan aiki tun 1982 ne aka nemi fara shi, amma abin ya kakare. Lokacin gwamnatin Jonathan an nemi a fara, bayan an sabunta yarjejeniya, amma anin ya sake kakarewa.

A wannan lokaci na Buhari kuma, batun ya tsaya cak, har sai wata daya kafin jawabin sa, aka sanya hannu a yarjejeniya da wani kafanin kasar Chana, wanda shi ne zai kashe kudin sa har kashi 85 bisa 100, yayin da gwamnatin tarayya za ta bada kashi 15 kacal.

Kwangilar dai a kan dala bilyan 5.7 za a yi ta domin samar da lantarki migawat 30,000.

TSINKAYE NA 6:

Ikirarin Buhari cewa harkar takin zamani ta inganta a lokacin sa, sabanin shekarun gwamnatin da ta shude.

Buhari ya ce an farfado da masana’antun takin zamani 11, ana samun buhunan taki har milyan 7, kuma an killace dala milyan 150 na kudin da akan sayi taki a waje da kuma kebe wasu dala milyan 60 na tallafi shigo da taki.

Ya kuma bayyana cewa farashin takin zamani ya fadi daga naira 13,000 zuwa naira 5,500 kowane buhu mai nauyin kilogiram 50.

Tabbas za a iya cewa wannan jawabi na Shugaba Buhari gaskiya ne, domin jarjejeniyar takin zamani da ya kulla da kasar Morocco ta haifi da mai ido.

Sai dai kawai har yanzu wasu manoman sun kasa yarda cewa farashin taki ya sauka daga naira 13,000 zuwa 5,500 cif-da-cif.

TSINKAYE NA 7

Ikirarin Buhari cewa darajar naira ta tsaya kyam da kafafun ta, inda ya ce tun daga Fabrairu, 2017 da ta tsaya a 360 ko 365 a kowace dala daya, naira ba ta sake yin tashin gwauro zabo kamar da da ta kan kai har naira 525 ba.

Wannan ikirari na Buhari gaskiya ne. Domin hukumar kididdiga ta kasa ta tabbatar da cewa tsadar rayuwa ta ragu da kashi 9 bisa 100, idan aka kwatanta da 2015.

Sai dai kuma wani abin dubawa shi ne, a loakcin da Buhari ya hau mulki, ana saida dalar Amurka a kan naira 199.5 ne.

TSINKAYE NA 8:

Buhari ya ce ya bai wa jihoji har naira tiriliyan 1.642 tsakanin 2015 zuwa yau, domin su biya basussukan albashi, kudaden fansho da kuma tallafawa wajen kafa kananan masana’antu, wadanda aka yi watsi da su shekara da shekaru.

Wannan ikirari na sa gaskiya ne kwarai kuwa: 2015 ya ba jihohi naira bilyan 200, sai naira bilyan 441 cikin 2016, da kuma naira tiriliyan 1 cikin 2017.

TSINKAYE NA 9:

Buhari ya ce Gwamnatin sa kashe naira bilyan 500 wajen shirin ciyar da dalibai, samar da aikin yin a N-Power, tallafin Iyali na FHF, shirin samar da gidaje masu saukin kudi, da sauran su.
Wannan ikirari shi ma gaskiya ne matuka.

TSINKAYE NA 10:

Buhari ya ce su na aiki tukuru wajen kakkabe illar cin hanci da rashawa a kasar nan. Ya ce sun takaita satar kudi ta tsarin shigo da asusun bai daya, TSA, tsarin fallasa wadanda su ka wawuri kudi, wato hura usur, killace bayanan biyan albashin ma’aikata da sauran su.

Wannan batu na tsarin TSA a gaskiya ba shi ne ya kirkiro shi ba. An kirkiro shi ne lokacin gwamnatin Jonathan. Don haka ba za a iya cewa wani sabon abu ne gwamnatin Buhari ta kirkiro.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ya zuwa Janairu 2015, sama da hukumomin gwamnati 500 su ka fara amfani da tsarin TSA, wanda aka shigo da shi tun cikin 2012.

Amma tsarin hura wa wadanda su ka wawuri kudin gwamnati usur, ana fallasa su, Shugaba Buhari ne ya kirkiro shi.

Share.

game da Author