Mai rikon kwaryan Shugabancin kungiyar ma’aikatan jinya na kasa, Stephen Lamiya ya koka kan yadda ba a mai da hankali wajen gyara asibitocin dake kula da cututtukan ido da kuma rashin samun horo da ma’aikatan asibitocin ke fama da su.
Stephen Lamiya ya fadi hakan ne a taron kungiyar da aka yi a Gombe ranar Talata inda ya kara da cewa asibitocin ido a Najeriya na fama da karancin ma’aikata.
Ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da na Jihohi su kara yawan ma’aikata a fannin sannan a inganta aiyukkan ma’aikatan ta hanyar basu horan da ya kamata.
Bayan haka wani kwararran ma’aikacin jinyar ido Musa Goyol ya yi kira ga gwamantin tarayya da ta gaggauta gyara asibitocin cewa bincike ya nuna mutane miliyan 285 a duniya na dauke da cutar ido sannan miliyan 39 daga cikin suna fama da makanta.
Ya ce mutane da dama a Najeriya na fama da cututtukan ido wanda ya hada da amosanin ido, Glaucoma da rashin samun ingantacciyar kula.