HARKALLAR NHIS: Sakamakon bincike ya nuna cewa Yusuf mailaifi ne – Ministan Kiwon Lafiya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya amince da da kara wa’adin dakatarwan da yayi wa shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa Usman Yusuf.

Ministan ya ce yayi hakan ne bayan Karanta sakamakon binciken badakalar bacewar wasu kudade da ake zargin Usman da aikatawa.

Yace sakamakon bincike ya nuna cewa Usman na da hannu dumu-dumu a harkallar saboda haka zai ba zai dawo aiki ba tukuna.

Adewole ya ce ya mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon binciken.

Idan ba a manta ba a ranar 5 ga wantan Yuli ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar inshorar kiwon lafiya ta Kasa ‘NHIS’ Usman Yusuf daga aiki.

Ma’aikatan kiwon lafiya na tuhumar Usman Yusuf da yin amfani da wasu kudade da ya kai naira Miliya 200 don gudanar da tirenin ga wasu ma’aikatan hukumar da kuma rashin jituwa dake tsakaninsa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewale.

Share.

game da Author