2019: Zan yi takaran shugaban kasa a PDP – Ibrahim Shekarau

1

Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya rubuta wa jam’iyyar PDP wasika ta musamman cewa ya na da bukatar shiga sahun masu neman shugabancin kasar nan a inuwar jam’iyyar PDP.

A wasika ta musamman da ya aika wa uwar jam’iyyar, Shekarau ya ce abin da ya sa bai fadi a gidajen jaridu cewa zai fito ba tuntuni, yana so ne ya fara sanar wa jam’iyyar kafin ya fito karara.

Darektan yada labaran tsohon gwamnan, Yau Sule ne ya sanar da haka wa manema labarai.

Yanzu dai shine mutum na uku a jam’iyyar da ya fito ya nuna ra’ayinsa na fitowa takarar shugabancin kasa Najeriya a jamiyyar PDP.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido sai yanzu Ibrahim Shekarau.

Share.

game da Author