2019: Kada fa ’yan siyasar Arewa su bari Fayose ya yi musu sakiyar da babu ruwa

0

An bayyana tsayawa takarar shugabancin kasar nan da Ayo Fayose, gwamnan jihar Ekiti ya yi, ya zama wani zaburaswa da kuma farkawa daga barcin siyasa da Arewa ke yi.

Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Filato Damishi Sango ya ce gwamna Fayose na bukatar kawai a fara motsa gangar kidan hauma-haumar siyasa ne, domin shi cin zabe fa ya na bukatar dogon lokaci mai tsawo ana shiri. Kamar yadda ake cewa ba a fafe gora ranar tafiya.

Ya kara da cewa da alama Fayose ya ji haushin yadda jam’iyyar PDP ta yi likimo ne, ba ta wani motsi, duk da kasancewa lokaci na ta karatowa. “Dalili kenan shi ya ce, tunda babu kowa, to shi ga shi ya fito.”

Haka Sango, wanda tsoohon ministan harkokin wasanni ne, ya furta yau Talata a Jos.

A cikin watan jiya ne dai Fayose ya kaddamar da aniyar sa ta neman tsayawa takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, har ya na shan alwashin kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a 2019.

Wannan fitowa da Fayose ya yi, ta janyo ka-ce-na-ce musamman a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki na PDP. Har ta kai ga jam’iyyar ta ce Fayose na bata lokacin sa ne, domin tikitin takarar shugabancin kasar nan na PDP, an rigaya an mika shi ga Arewacin kasar, daga can dan takarar zai fito.

Shi dai Fayose dan yankin Kudu-maso-Yamma ne.

Sango ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN cewa Fayose wani kalubale ne ya yi wa Arewa.

“Na san tabbas jam’iyya ta bayar da tikitin ga Arewa, amma hakan fa ba zai hana wani daga wani yanki ya fito ya nuna bukatar sa ba.

“Idan ‘yan siyasa daga Arewa sun nuna rashin bukata ko rashin sha’awar su ta tsayawa takara, ai kenan sai wasu daga wani yanki su fito, kuma su nemi mu amince da su.’’ Haka Damishi ya bayyana.

Daga nan sai ya yi kira ga masu sha’awar takara daga Arewa da su fito tun yanzu da wuri domin a san da su, su motsa jam’iyya. Ya na mai cewa a zaben 2019, PDP ba ta tsoron karawa da jam’iyya mai mulki, APC, kuma ba ta tsoron cewa wai don ta na mulki, to mai layya shi ke da nama.

“Allah ya kai mu 2019 lafiya, a fito a fafata, mun yi shirin kokawar neman cin zabe a kowane mataki.”

Share.

game da Author