2019: Dokoki 9 da Jam’iyyu zasu kiyaye – Hukumar Zabe

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ya gargadi ‘yan siyasar da su ka yi azarbabin fara kamfen tun yanzu da cewa sun tafka kuskure, kuma sun karya dokokin zabe.

Mahmood Yakubu ya yi wannan gargadi ne yayin da ya ke taron ganawa da jam’iyyun siyasa na kasar nan, a Abuja. Taron dai wanda ya saba gudanarwa ne duke bayan watanni uku.

Bayan haka yayi karin bayani kamar haka:

1. Ana fara kamfen kwanaki 90 kafin ranar zabe, a daina sa’o’i 24 kafin a fara jefa kuri’a.

2. Jam’iyyu su ja kunnen wadanda su ka fara kamfen, duk da mun san ba a karkashin jam’iyya su ke yi ba, kowa shi ke tallata kan sa. Amma ai kowa ya na da jam’iyyar da ya ke, tunda ba mu da Dan Takara na Indifenda a Nijeriya.

3. Har yau jam’iyyu 18 ba su nada Shugabannin Kwamitin Gudanarwa na Kasa ba, NEC. Rashin yin hakan kuwa an kauce wa doka ta 223.

4. Jam’iyyu 28 ne daga cikin 46 su ka cika wancan sharuddan nada Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na Kasa.

5. Tilas sai jam’iyya ta bude ofis a Abuja: Amma jam’iyyu 17 ne ke da ofs a Abuja, saura 22 kuma ba su kai ga budewa ba.

6. Yayin da wasun su kuma kudin hayar da su ka kama ofis din ya kare, sun kasa biya, sai bilunbituwa su ke yi.

7. Har yau jam’iyyu 5 ne kacal su ka kai wa INEC bayanin yadda su ka kashe kudade a yakin neman zaben 2015. Sauran jam’iyyu 24 kuwa sun yi mirsisi.

8. Akwai wasu sabbin jam’iyyu 17 da za mu iya yi wa uziri, saboda an yi musu rajista ne bayan zaben 2015. Don haka ba ruwan su da gabatar mana yadda su ka kashe kudade a 2015, tunda ba da su aka yi zaben ba.

9. Akwai wasu jam’iyyu 108 da a yanzu haka ke neman a yi musu rajista. INEC za ta yi wa duk jam’iyyar da ta cika sharuddan da doka ta tanadar.

PREMIUM TIMES ta ruwaito Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ce shugaban INEC ya gargadi jam’iyyun da su cika wadannan sharudda domin zama cikakkun jam’iyyu.

Share.

game da Author