ZIYARAR ALI MODU OFISHIN OSINBAJO: Basu hadu da Oyegun ba – Jam’iyyar APC

0

Shugaban Jam’iyyar APC ya karyata labaran da ake ta yadawa wai an ganshi a fadar shugaban kasa a lokacin da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP Ali Modu Sherrif ya ziyarci mataimakin shugaban kasa.

A wata sanarwa da ta fito daga shelkwatra jam’iyyar a Anuja, APC ta ce shugaban ta John Oyegun bai tafi fadar shugaban kasa ranar da aka ce wai Sheriff ya tafi ba.

” Ko da yake ya tafi fadar shuagabn kasan, iyakan sa ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari.

APC tace wasu ne kawai ke neman ruruta wutar da bata ganin cewa siyasa ta kunno kai domin su kawo rudani a jam’iyyar a Jihar Barno.

Share.

game da Author