Za a yi wa yara Miliyan 1 alluran rigakafin cutar Kwalara a jihar Barno

0

Wani jami’a Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO, Wondi Alemu yace za su hada hannu da gwamnatin Najeriya don yi wa yara miliyan daya alluran rigakafin cutar kwalara a jihar Borno.

Wondi Alemu ya ce kamfanin sarafa magunguna na GAVI, kungiyoyin da ke bada tallafi da kungiyar WHO sun ba Najeriya alluran rigakafin cutar kwalara 915,005.

Ya kuma kara da cewa za su yi aiki da hukumar NCDC da ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Borno domin yin alluran ga yara kyauta a jihar musamman a wuraren da cutar ta fi yawa.

Ya ce an fara yin alluran rigakafin tun ranar 18 ga watan Satumba sannan za a ci gaba har zuwa wasu ‘yan kwanaki masu zuwa.

An fara yin alluran ne a sansanin ‘yan gudun hijra dake Muna da kananan hukumomin Jere, Monguno da Dikwa.

Wondi Alemu ya ce kungiyar WHO za ta hada guiwa da hukumar UNICEF, hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya da sauran kungiyoyi wajen fadakar da mutane game da illollin cutar kwalara da hanyoyin da za a bi don samun kariya daga cutar.

Share.

game da Author