Za a bude sashen Jami’ar Kaduna da aka rufe a kudancin jihar

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya ce za a bude sashen jami’ar Kaduna dake kudancin jihar.

Kakakin gwamnan Samuel Aruwan ne ya sanar da haka bayan ganawa da El-Rufai yayi da wasu yan yankin da suka kawo masa ziyara fadar gwamnati.

Ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta rufe sashen jami’ar dake kudancin Kaduna din ne saboda rikicin da akayi ta samu a yankin kwanankin baya.

Bayan haka kuma gwamnatin tace zata bude wani sashe na jami’ar a kowani karamar hukuma a jihar.

El-Rufai yace za a yi haka ne domin nan gaba su iya zama jami’o’i masu zaman kansu.

Share.

game da Author