Yawan yaran da ke dauke da cutar Kenda ya karu a Najeriya

0

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ta ce adadin yawan yaran da basu sami allurar rigakafin cutar kenda a Najeriya ya karu daga shekara 2014 zuwa 2016 musamman a arewacin kasar.

UNICEF ta fadi haka ne a taron wayar da kan mutane da aka yi kan mahimmancin allurar rigakafin cutar kenda a Abuja ranar Alhamis inda ta kara da cewa Najeriya ta fi yawan yaran da basu samu yin alluran rigakafin cutar na farko a duniya ba.

A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na kasa Faisal Shuaib ya ce a lissafe an sami adadin yara da suka kamu da cutar kenda a Najeriya ya karu daga miliyan 190 a shekarar 2014 zuwa miliyan 527 a shekarar 2016.

Wata Jami’a a UNICEF Margaret Adaba ta ce yawan yaran da ba su sami alluran rigakafin cutar kenda a Najeriya ya kai miliyan 3.3 sannan kasar India na biye mata da yawan yaran da suka kai miliyan 2.9.

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko, Faisal Shuaib ya ce gwamnatin tarayya na shirin wayar da kan mutanen kan mahimmancin alluran rigakafi domin a yanzu haka gwamnatin ta samar da Naira biliyan 3.5 domin hakan.

Faisal ya yi kira ga jihohin kasar nan da su mara wa gwamnatin tarayya baya wajen yin irin haka a jihohinsu.

Share.

game da Author