Jam’iyyar PDP ta ce ba sai ka yi wa yan Najeriya iso ba kuma game da ko za suyi APC ko A’a domin jiki magayi.
Kakakin jam’iyyar Dayo Adeyeye ne ya fadi haka inda ya kara da cewa in banda karerayi da jam’iyyar take tayi wa jama’a babu wani abin azo a gani da ta tabuka tun hawanta.
” Bari in tabbatar muku cewa da irin wadannan abubuwa da APC ta ke cewa tayi ne zamu ci zabe domin batayi komai ba koma jama’a sun sani.
Ya ce kafin APC su karbe mulki, ana siyar da buhun Shinkafa 8,000 ne amma yanzu fa? sannan sun yi abubuwa da dama wanda da zuwan APC komai ya wargaje.
” kullum sai kaji suna cewa PDP ce ta lalata kasa bayan har yanzu basu yi abin da yafi na PDP din ba.”