‘Yan Majalisa na kara yi wa Sanata Saraki da Ekweremadu tofin Allah wadai

1

Ana ci gaba da samun karin ‘yan majalisar tarayya masu yi wa Shugaban Majalisar Dattawa tofin Allah-wadai.

Hakan ya biyo bayan furucin da ya yi a makon da ya gabata, inda ya ce haramun ne sojoji da Gwamnonin Kudu-masu-Gabas su haramta kungiyar Biafra.

Jim kadan da yin bayanin na sa, Hon. Ado Doguwa ya fito ya ragargaje shi, ya na mai cewa wannan kasassaba ce kawai ta bulkarar siyasa Sanata Saraki ya yi.

A yau kuma sai ga wani gungun mambobin majalisar tarayya da su ka hada da; Hon. Aliyu Madaki, Mohammed Soba da Sani Zorro, su ka fito a karkashin kungiyar mambobin majalisa masu neman kawo ci gaba, su ka la’anci Sanata Saraki.

Cikin takardar da su ka raba wa manema labarai, sun bayyana cewa, ta tabbata dai maitar Saraki ta fito fili, domin a takaice ya nuna ya na goyon bayan tsagerun Biafra. A haka sai su ka ce ba abin mamaki ba ne, domin biri ya yi kama da mutum.

Haka kuma, da su ka karkato kan Mataimakin Saraki, Sanata Ike Ikweremadu, gamayyar mambobin majalisar sun tunatar wa ‘yan Najeriya yadda Ikweremadu ya maida Nnamdi Kanu shalelen sa, jim kadan bayan an bayar da belin sa.

Sun bayyana cewa baya ga ziyara da ya kai wa Kanu, har amfani da jami’an tsaron sa da motocin da gwamnati ta ba shi ya na hawa sai da ya yi a wajen yi wa Nnamdi Kanu hidima.

Share.

game da Author