Shugaban Kwamitin bai wa Shugaban Kasa Shawara a kan rashawa da cin hanci, Farfesa Itse Sagey ya bayyana mambobin Majalisar Dattawa da ta Tarayya a matsayin masu shanye jinin talakawa, kuma farin dangon da ke cinye shukar talakawa.
Farfesan ya yi wannan furuci ne, wanda ya sha yi a baya, a wurin wani taron masu ruwa da tsaki a Cibiyar Mazarin Harkokin Kasashen Waje, da ke Victoria Island, Lagos.
Sagey ya ce ba su da wani amfani sai cinye bilyoyin nairorin da ya kamata a ce an yi wa jama’a aiki da su.
“Duk makaryata ne, dibgaggu, matsiyata, marasa imanin da ba su kishin jama’a sai kishin manyan aljifan su kawai.”
Ya yi tir da har yau babu wanda ya san iyar adadin tulin kudaden da su ke kwasa a duk wata, ko shekara, saboda sun ki bayyanawa don kada ‘yan Nijeriya su farga da irin babbar asarar da ake yi a duk wata ko shekara wajen raka asara da guda, ana damfara biyoyin kudade ha wadanda ba su da wani amfani ga ci gaban kasar nan.
Kafin nan dai sai da kakakin yada labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Abdullahi ya yi tir da irin halayyar Farfesa Sagey, wanda ya ce saboda rashin iya aikin sa ma bayar da ingattacciyar ha gwamnati, sai kayar da gwamnatin ake ta yi a wurin shari’un da suka danganci cin hanci da rashawa.
Shi kuwa Sagey, ya kara da cewa baya ha alawus-alawus na ‘yan majalisar, akwai makudan da sai irin su Honourable Jibrin da aka dakatar ne kawai zai iya fada maka abin da su ke samu.
“Bai kamata ma ana kiran su Masu Girma ba, tunda ba su da kima ko mutuncin tausayin al’umma.”