Wasu yan bindiga da ba a san ko suwaye ba sun kashe sarkin Gyangyan Mohammed dake masarautar Jhar, karamar hukumar Kanam Jihar Filato.
Iyalan mamacin sun sanar wa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, ‘yan bindigan sun shigo unguwan ne dauke da muggan makamai inda suka tafi kai tsaye zuwa gidan sarkin sannan suka bude masa wuta.
Sun kara da cewa a wannan lokaci da suka aikata wannan aiki, sun ajiye wasu yan uwansu a waje domin aikawa da duk wani wanda ya tunkaro kusa da gidan lahira.
Shugaban karamar Hukumar Kanam, Hayatu Bale ya ce sun sanar wa hukumar ‘yan sanda abin da ya faru.
Mutanen dai sun shigo unguwar ne da karfe 1 na safiyar Juma’a.