Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Sharrafaden Ali, ya tsallake rijiya da baya a yau Litinin, yayin da wasu ‘yan bindiga su ka bude wuta a Fadar Sarkin Ibadan, Olubadan na Ibadan a Popo-yemoja, Jihar Oyo.
Ali ya tsallake rijiya ne, tare da wasu ‘yan jarida uku, wadanda su ka je fadar domin su dauko labaran bikin rantsar da wasu hakimai hudu da Olubadan Saliu Adetunji zai yi.
Ganau ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigar sun zo fadar ne a cikin wata mota kirar Sienna, mai launin baki da misalin karfe 11:45 na safiyar yau.
Su na dira su ka fara ihu su na surfa wa bakin da ke cikin fadar zagi da harshen Yarbanci. Sannan kuma suna cewa duk mai iya tunkarar su ya fito idan ya isa.
Ali, wanda shi ke rike da sarautar Asiwaju Balogun na Ibadan, ya isa wurin a lokacin da aka fara harbe-harbe a fadar. Hotuna sun tabbatar de cewa harsasai sun ratattaka gilasan motar tasa kira Toyota Land Cruiser Jeep.
Akwai wasu ‘yan jarida uku da su ka samu kananan raunuka.
Idan ba a manta ba, cikin makon da ya gabata ne Sarkin na Ibadan ya kai gwamnan jihar kara, inda ya kalubalanci sabuwar dokar mallakar feguna da gonaki a jihar Oyo.
Discussion about this post