YAJIN AIKIN LIKTOCI: An kwana ana tattaunawa, amma ba a haifi da mai ido ba

0

Duk da kwana da mambobin kungiyar ma’aikatan likitocin Najeriya suka yi suna tattaunawa kan ko zasu amince da alkawurran da gwamnati ta yi wa likitocin don janye yajin aikin da suke yi, abin ya ci tura domin har zuwa karfe bakwai na safen Laraba ba su kai ga matsaya ba.

Wakiliyar mu Nike Adebowale ta ruwaito mana cewa shugaban kungiyar ya ta tafi ma’aikatar kiwon Lafiya domin ganawa da ministan Isaac Adewole inda ake sa kyautatat zaton za su ci gaba da zama da karfe 10 safen yau.

Share.

game da Author