Mutanen jihar Zamfara sun fada cikin matsanancin rashin ruwa saboda yajin aikin da kungiyar kwadugon NLC reshen jihar ta shiga.
Kungiyar NLC ta gudanar da yajin aikin ne saboda rashin biyan hakokkin ma’aikatan jihar da gwamnatin ta ki yi wanda ya hada da rashin biyan su albashin ma’aikata 1,400 da ta dauka tun a shekarar 2014, rashin kara yawan ma’aikata musamman ganin cewa wasu sun yi ritaya wasu kuma sun canza wajen aiki. Bayn haka kuma wasu ma’aikatan har yanzu na karban albashin su kasa da Naira 18,000 da kuma sauran su.
Kamfanin dillancin labarai ta rahoto cewa mutanen jihar da dama musamman mazauna Gusau na neman ruwan sha wurjanjan saboda shiga yajin aikin da hukumar samar da ruwan sha ta jihar ta shiga.
Yajin aikin ya shafi har da gidajen talabijin da na rediyon jihar.
Discussion about this post