Rundunar ‘Yan sandan Jihar Bauchi ta bada sanarwar cafke mutane hudu da ake zargin sun yi wa tsohuwa mai shekara 70 dukan da ya yi sanadiyyar ajalin ta.
An kashe tsohuwar ne a kauyen doka da ke kusa da garin Bauchi, bayan an zargi tsohuwar da maita.
Kakakin ‘yan sandan jihar, Kamal Mohammed, ya bayyana cewa an kashe tsohuwar mai suna Liyatu Micheal ranar 5 Ga Satumba, 2017.
“Wadanda mu ka kama sun zargi Liyatu tare da wata gyatumar su biyu da laifin maita. Daga nan su ka ja su zuwa wani daki, inda su ka rufe su da duka.
” Yayin da suka farga cewa Liyatu ta mutu, sai suka dauko gawar ta su ka ajiye a bayan gida, su ka tsere.’
Kakakin ‘yan sandan ya ce ita kuwa daya tsohuwar mai suna Keziya, ta ci dukan tsiya, amma ba ta kai ga mutuwa ba, aka garzaya da ita asibiti.
“Mun kama wadanda ake zargi da yin dukan har su hudu. Amma har yanzu mu na neman sauran wadanda suka tsere.
Ya ce ba da dadewa ba za a gurfanar da su kotu, domin yi musu hukunci na daidai laifin da ake zargi sun aikata.
Wata majiya a kauyen Doka ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana zargi Liyatu da Keziya da laifin maita ta yadda ake samun mutuwar daidaikun mutane a garin.
“Bayan an tunkare su da wannan zargi, sun yi ikirarin cewa lallai su na yin maita. Sannan ita Liyatu ta ce ita ce ta jefa wa wata maijego kurwar rashin lafiya tun bayan haihuwar da ta yi.”
Majiyar mu da ta roki a boye sunan ta, ta ce maijegon mai suna Yelkon, ta kasance kwance ba lafiya tun bayan da Liyatu ta furta cewa: “Za ki yi rashin lafiyar da ba za ki sake tashi ba, har karshen rayuwar ki.”
Discussion about this post