Sanata mai wakiltan Kaduna ta Arewa kuma jigo a siyasar Kaduna ya ce babu abinda zai sa ya mara wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai baya a zaben 2019.
Ya ce ya yanke wannan shawara ce ganin irin abubuwan da gwamnan yake yi na nuna halin ko in kula da yin abinda ya ga dama da jam’iyyar a jihar mai makon ayi don jama’ar da suka zabe su.
Sule ya fadi haka ne a wata hira da yayi ta musamman da gidan jaridar Sun da wallafa yau.
Yace idan har ma El-Rufai zai yi takara a 2019, to iya ruwa fidda kai.
” Daya daga cikin dalilan kuwa shine ganin yadda mutanen jihar Kaduna ke bukatar sauyi, saboda haka ni Sule ba zan ki jama’a ba ko in yi musu tawaye domin ni na jama’a ne.
” Amma idan har yayi nadama, ya ce zai dawo ya rike jama’a ya nuna kowa nashi ne, ya nemi gafara, tabbas zamu bi inda jama’a suke ne. ”
Yanzu lodin na neman yayi wa El-Rufai yawa. Barakar dai sai dada budewa takeyi inda ake ta samun wadanda ake zaton suna tare suna nuna ba sa tare yanzu.
Discussion about this post