Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa yanzu ta samu ikon kama ‘yan kungiyar matasan nan da suka ba ‘yan kabilar Igbo wa’adin 1 ga watan Oktoba su tattara nasu-i-nasu su koma yankinsu.
Ya roki mazauna jihar da su sanar da ‘yan sanda duk inda suke kaganin za a ga dayansu ko kuma gidajensu.
Gwamna El-Rufai ya fadi haka ne a wata takarda da kakain fadar gwamnatin Samuel Aruwan ya saka wa hannu a garin Kaduna.
Tun a watan Yuli da kungiyar matasan Arewa suka ba yan kabilar Igbo mazauna Arewa su koma garuruwansu ne El-Rufai ya sanar cewa sai ya taso keyar wadannan matasa da shugabannin kungiyoyin da suka sa hannu a takardar.
Mutane sun fito sun nuna fushinsu akan wannan himma na gwamna El-Rufai cewa tunda kungiyar tsagerun Biafra suke yi ta muzguna wa ‘yan Arewa bai tab nuna fushinsa ko ya fito yayi nuna rashin giyon bayansa akai ba sai da matasan Arewa suka fito suka fadi nasu matsayar.
El-Rufai ya zaiyanu bayanai da sashen da ya ba shi ikon kama wadanna matasa da gurfanar dasu a gaban kuliya.