Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, za ta sake garzaya kotu gobe Alhamis, domin neman sabon umarni, sanadiyyar yadda Sanata Dino Melaye arce daga ofishin sa a Majalisar Dattawa, domin kada ya karbi takardun bayanan korafin neman yi masa kiranye.
Yammacin ranar Talata ne jami’an INEC suka dira Majalisar Dattawa da nufin damka wa Melaye takardun korafe-korafe da bayanan shirin fara yi masa kiranye.
Ganin yadda yak i yarda ya karbi kwafen takardun, sai jami’an INEC su ka jibge su a bakin ofishin sa. Sai dai kuma a lokacin ma ofishin a rufe ya ke. rahotnni sun ce a lokacin da jami’an INEC su ka isa, Melaye ya na cikin zauren majalisa a zaune.
Amma kakakin yada labaran INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce ba zai yi magana a kan batun da ke gaban kotu ba, ko kuma abu da ya shafi fannin shari’a.
PREMIUM TIMES ta samu tattaunawa da Daraktan Wayar da Kai kan Katin Rajista, Oluwaole Ozzi, wanda y ace Dino Melaye tserewa ya yi daga ofis, domin kada a damka masa takardun. Ya kara da cewa hukumar zabe za ta kama shi kotu a gobe Alhamis, dangane da arcewar da ya yi.
“Mun yi kokarinmu don mu ga mun damka masa, amma ya zudu.” PREMIUM TIMES ta ga ofishin Dino mai lamba 2:13 a kulle.
Ganin yadda jami’an hukumar zabe suka dira majalisar, jama’a sun yi cincirindo domin su ga yada za a karke idan ya fito daga majalisa. Fitowar sa ke da wuya, an fada bin sa, sai ya yi sauri-sauri-gudu-gudu ya fada mota.
Premium Times Hausa ta fahimci jikin Melaye ya fara sanyi, domin a ranar Lahadi, yay i amfani da shafin san a Twitter ya nuna cewa, “ga Allah mu ka dogara, ba ga dan Adam ba.” A kuwa, daga cika-baki sai hargagi da bugun kirji kawai yak e yadawa a cikin shafin.
Hukumar zabe dai za ta fara shirye-shiryen yi wa Sanata Melaye kiranye a farkon satin Oktoba.
Discussion about this post