TSAKANIN SOJOJI DA IPOB: An saka dokar hana walwala a jihar Abia

0

Gwamnatin jihar Abia ta saka dokar hana walwala a garin Aba sanadiyyar rikici da ya barke tsakanin magoya bayan mai fafutikar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, wato IPOB da Sojojin Najeriya da suke atisayi a garin na Aba.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin Jihar ta ce dokar ta fara aiki ne daga karfe 6 yamman yau Talata zuwa ranar 14 ga watan Satumba.

Babu fita ko zirga zirga a garin Aba daga Karfe 6 yamman Talata.

Gwamnan jihar Okezie Ikpeazu, ya ce ba za su sa ido su bari wasu na neman tarwatsa hadin kan Najeriya ba.

Share.

game da Author