Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce zata gudanar da bincike akan rikicin da yan daban siyasar magoya bayan gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da na tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso wanda yayi sanadiyyar tada zaune tsaye a lokacin da ake hawan Daushe a Kano.
Idan ba a manta ba magoya bayan Ganduje da na Kwankwaso sun ba hammata iska a Kano a wajen hawan Daushe inda da yawa daga cikin magoya bayan yan siyasan suka sami munanan raunuka.
Kakakin rundunar, Magaji Majiya ya ce rundunar ba za tayi kasakasa ba wajen kamo wadanda suka tada da wannan fitina da kuma tabbatar da an hukunta su.
Yayi kira ga mutanen gari da su zauna lafiya tsakaninsu sannan su sanar da yan sandan duk abinda ke neman jawo tashin hankali a unguwannin su.
Discussion about this post