TATTALIN ARZIKIN KASA: Inga talaka na wal-wala shine fita daga wannan kangi- Inji Buhari

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce fita da Najeriya ta yi daga halin tabarbarewar tattalin arzikin Kasa da aka ruwaito abu ne mai kyau amma ganin talaka ya ji hakan shine abin da ya kamata.

Buhari ya fadi hakan ne da ya ke karbar bakuntar shugaban kasar Nijar Muhammadu Issofou a garin Daura.

Ya ce yana matukar farincinkin jin hakan amma yaga talaka da wal-wala shine yafi masa. Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba kokarin ganin an samu wal-wala  da wadatan arziki a kasa baki daya.

Da yake ya da ta sa zancen, shugaban Nijar ya ce ya taho garin Daura ne domin ya duba lafiyar Shugaba Buhari sannan su tattauna game da kasashen nasu biyu musamman tattalin arzikin Kasa da tsaro.

Share.

game da Author