Tasirin da Fasahar Kimiyya Ya Aiwatar Wajen Bunkasa Tattalin Arziki da Zamantakewa, Daga Ahmad Usman

0

An bayyana tasirin da ilmin kimiyya da fasaha suka aiwatar cikin shekarun da suka gabata da ‘gagarumin’ sauyi wajen bunkasa tattalin arziki da sana’o’I da ilmi da kiwon lafiya da kuma zamantakewar al’umma.

Aminu Kabir, wani dalibi daga Jami’ar Birmingham City da ke qasar Ingila ne ya bayyana haka a wajen taron qarawa juna sani na yini guda da kungiyar daliban masarautar Jama’a da ke cikin jihar kaduna (JESA) ta shirya wanda aka gudanar da shi a dakin taro na ‘Women Multi-Purpose Center’ da ke garin Kafanchan cikin karamar ramar hukumar Jama’a da ke kudancin jihar Kaduna.

Kabir, ya bayyana cewa waxanda basu fahimci alfanun da irin wannan fasaha ya haifar ba suna yin haka ne kawai sakamakon irin bahaguwar fahimtar da su ka yiwa lamarin ta inda suke cewa ya ragewa al’umma ziyartar juna da rashin sadar da zumunci.

“Mutane nawa suka kulla zumunci a sakamakon hanyoyin sadarwa na zamani da fasahar kimiyyar zamanai ta samar?

Mutane nawa suka mallaki takardun digiri har ma da digirin digir-gir a wata qasa daga gidajensu ba tare da sun sha wahalar tsallakawa zuwa kasar ba?” in ji shi

Aminu Kabir ya kara da bayyana cewa bisa ga wani bincike da aka gudanar kwanan nan a kasar Amurka ya nuna cewa daliban da ke koyon karatu kai tsaye ta hanyar sadarwa ta intanet sun fi kwarewa da fahimta fiye da daliban da ke karatu cikin azuzuwa zaune a gaban malamansu.

“Cikin sauri an samu saukin gudanar da rayuwa. Maimakon aikewa da sako ko jiran sako ta hanyar akwatin gidan waya cikin ‘yan dakikoki kawai za ka aike ko kuma karvar saqo ta hanyar Imel. Duk da cewa ba za a kaucewa kirga illolin da suka haifar ba, amma kuma dole a sallamawa ci gaban da suka samar.” Ya karkare.

Shi kuwa a na shi jawabin, Dakta Musayyib AbdulMajid, likita daga babban asibitin gwamnati da ke karamar hukumar Kauru ta jihar kaduna, wanda ya gabatar da mujalla mai taken ‘Illolin Shaye-Shaye’, ya bayyana cewa harjar shaye-shaye, wanda ya zama rowan dare tsakanin kowane rukunin maza da mata, dalibai da marasa aikin yi abin takaici ne.

“bincike ya nuna a tsakanin mutane miliyan 162 zuwa miliyan 324 wanda ya kunshi kashi 3.5 zuwa kashi 7.0 na mutanen duniya da shekarunsu ya kama daga 15 zuwa 64, tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013, sun taba yin tu’ammuli da harkar kwaya,” in ji shi.

Dr. Musayyib ya bayyana cewa sau da yawa kawaye da abokai ke fara tallatawa mutum ra’ayin shaye-shaye musamman idan sun laqanci yana cikin wani hali na damuwa.

“Wani lokaci kuma dalibai da ke karatu a manyan makarantu ke fara nunawa ‘yan uwansu dalibai cewa in har suna so su rika samun tunani mai kyau da natsuwa wajen fahimtar karatu sai suna haxawa da shaye-shaye wanda kafin a Ankara sun zurma aboki ko qawa cikin harkar maye.”

“Sau da yawa mutum yak an fara ne da kadan-kadan amma kafin ya Ankara tuni ta riga ta aure shi sai kuma munanan sakamako su fara bayyana a hankali wanda a qarshe in ba a yi sa’a bas hike nan mutum sai ya zautu ya zamo mara amfani a cikin al’umma.”

Shugaban kungiyar, Zahraddin Khairu Ladan ya bayyana makasudin shirya irin wannan taro da cewa suna yin sa ne a bayan kowace karama da babban salla ga daliban masarautar da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandiri a sassan kasar nan don kara karfafasu a kan dagewa da neman ilmi da kuma nuna musu illolin miyagun dabi’un da ake koyowa a manyan makarantu.

Share.

game da Author