TARON MAJALISAR ZARTASWA: Manema labarai sun yi wa Aisha Alhassan caa a fadar Shugaban kasa

1

Manema labarai da masu daukan hoto a fadar shugaban kasa sun yi wa ministan Mata Aisha Alhassan bin kudan zuma don daukan ta hoto ganin ta halarci taron majalisar zartaswa na mako-mako da ake yi a fadar shugaban Kasa.

Ganin cewa ba da dadewa ba ministan ta bayyana mubaya’arta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar in da tace ko Buhari ya fito takara a 2019 ba za tayi shi ba, Atiku za tayi.

Wasu da dama daga cikin magoya bayan Buhari da gwamnoni sun yi kira ga ministan da ta ajiye aikin ta dalilin haka.

Share.

game da Author