TAMBAYA: Wani suna ne Ismullahil-A’azam cikin sunayen Allah
AMSA:Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Malamai sunyi sabani akan wane suna ne Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma) Shin akwai Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma) ko babu?
KAULI NA FARKO
Malaman wannan kauli sun tafi ne akan cewa babu Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma). Domin babu fifiko a cikin sunayen Allah, dukkan sunayensa masu girma ne da daraja, kuma girmansu da darajarsu daya ne, babu wani suna daga cikin sunayen Allah da yafi wani. Bugu da kari ma bai halatta ba a kudurce cewa wani suna daga cikin sunayen Allah yafi wani ba, ko a fifita wani suna akan wani.
Masu wannan fahimta daga cikin malamai sun fassara hadisan da suka zo da Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma) da wannan ma’anoni:
1 – “Sunan Allah Mai Girma” domin kowanne daga cikin sunayen Allah zaka iya siffantashi da “Mafi Girma”. Kenan dukkansu masu Girma ne kuma kowannen su Mafi Girma ne.
2 – Ko kuma a ce Hadisan suna nufin yawan lada ga dukk wanda ya yayi amfani da wadannan sunayen da aka ambata a cikin Hadisan.
3 – Ko kuma a dauka cewa ma’anan wadannan Hadisan shi ne, dukk mutumin da ya roki Allah da wani suna daga cikin sunayensa, a halin tsananin kadaita Allah da ikhlasi ga Allah. Wannan yanayi na tsananin ikhlasi ga Allah shi ne Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma).
Malaman sun kara da cewa, duk Hadisan da sukayi Magana akan Ismullahil-A’azam (Sunan Allah Mafi Girma), suna nufin daya daga cikin wadannan ma’anoni ne, domin babu wani suna da akekiransa da Ismullahil-A’azam (Sunan Allah Mafi Girma) shi kadai. Wadannan malamai sun kara da cewa Hadisan da suka ambaci Ismullahil-A’azam (Sunan Allah Mafi Girma) basu ayyana wani suna guda daya rak ba, sun ambaci sunaye da zikirori ko ayoyi daban – daban. Sabo da haka musu goyon bayan wannan fahimta suke cewa dukk sunayen Allah masu germa ne, masu falala ne, masu alfarma ne, masu daraja ne kuma duk siffofin ne na Allah ba za’a fifita wata siffa akan wata ba.
Malamai masu wannan fahimta sun hada da Abu Ja’far al-Dabari, Abul Hassan al-Ash’ari da sauran su.
KAULI NA BIYU
Malaman da sukace akwai Ismullahil – A’azam (Sunan Allah Mafi Girma).
Kuma suma sun kasu gida biyu:
1) Malamalan da suka tabbatar da akwai Sunan Allah Mafi Girma (Ismullahil-A’azam), amma fa suka ce, babu wanda ya sanshi, domin Allah yabarma kansa sanin wannan suna, kuma bai sanar da kowaba a cikin bayinsa.
2) Na karshe, sune malaman da suka tabbatar da akwai Sunan Allah Mafi Girma (Ismullahil-A’azam), kuma suka ayya lafazinsa. Sai dai suma sun samu sabani akan mene ne hakikanin Ismullahil-A’azam (Sunan Allah Mafi Girma). An kawo zantuka guda goma sha hudu akan Sunan Allah Mafi Girma.
Kowane suna daga cikin wadannan akwai masu cewa shi ne Sunan Allah Mafi Girma (Ismullahil-A’azam):
1 – Allahu
2 – Allahur Arrahmanur Rahim
3 – Arrahmanur Rahimul Hayyul Qayyum
4 – Al- Hayyul Qayyum
5 – Al-hannaul Mannanu Badi’us Samawati wal Arda, Dhu-Jalali wal Ikramil Hayyin Qayyum
6 – Badi’us Samawati wal Arda, Dhu-Jalali wal Ikram
7 – Dhu-Jalali wal Ikram
8 – Allahu la ilaha illa Huwa, al-Ahadus Samadul Ladhi lam yalid walam yulad walam yakullahu kufuwan ahad
9 – Rabbi Rabbi
10 -La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin
11 – Huwa Allahu Allahu Allahul ladhi la ilaha illa Huwa Rabbul Arshul Azim
12 – La ilaha illallah
13 – Huwa
14 – Daya ne daga cikin Sunaye 99.
Ibnu Qayyim ya ruwaito cewa ma’abuta ilimi duk sun karkata akan cewa Sunan Allah Mafi Girma (Ismullahil-A’azam) shi ne “ALLAHU”. Suka ce shi ne sunan da ya game dukkan sunayen Allah da siffofinsa.
Shi ne sunan da ba’a kiran wani da shi sai Allah, kuma shi ne sunan da aka ambata a AL-Kur’ani sau 2360, bugu da kari ma duk sauran sunayen da aka ambata suna shigewa cikinsa ne ko kuma akwai sa a ciki. Bayan Allahu kuma sai Al-Hayyul Qayyum.
Allah Shi ne Mafi Sani.
Discussion about this post