TAMBAYA: Menene yasa mutumin da ya rasa Sallar Juma’a sai yayi Azabar – Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Menene yasa mutumin da ya rasa Sallar Juma’a sai yayi Azabar. Menene ya hada Sallar Azahar da Juma’a

2- shin mutanen da suka rasa Sallar juma’a za su iya yin jam’in ta a Masallacin ko a’a.

3 – shin Sallar Juma’a dai dai take da Sallar Azahar. Ko kuwa ko wanne matsayinsa da bam. Sannan me ya sa ba a rama ta sa ace wai ayi Azahar.

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Duk mutumin da ya rasa Sallar Juma’a domin uzuri da shari’a ta yadda da shi, to zai sallace Azzahar a mamadin ta kuma a lokacinta ranar Juma’a. Bai halatta ya jinkirta ta ba har lokacin Azzahar ya fita, balle kuma ya kaita ranar assabar. Wanda kuma baiyi Sallar Juma’a ba, batare da uzurin da shari’a ta yadda da shi ba, to ya yi gaggawan tuba zuwa ga Allah kuma ya Sallaci Azzahar.

Sallar Juma’a tanada alaka da azzahar, domin azzahar ita ce asalin sallar Juma’a. kuma ana yin Juma’a ne a mamadin ta, a cikin lokacin ta.

Juma’a tanada ka’idoji da sharudda, duk mutanen da suka rasa juma’a baza su yi ta ba, saidai su yi azzahar a cikin jam’i.

Juma’a tana maye gurbin azzahar ranar juma’a, amma idan aka rasata, to, sai a sallaci azzahar. Abinda ya sa ba a rama juma’a da sallar juma’a shi ne ita juma’a tanada manufofi da dalilan da shari’a ta shar’anta ta. Irin taruwan jama’ar gari guri guda, fadakarwa, sannayya da taimako, bugu da kari dunkulewa da yenta a guri daya kuma lokaci daya wata alamace daga cikin alamomin musulunci.

Allah shi ne mafi sani.

Share.

game da Author