TAMBAYA: Ko malam zi yi mana Karin Bayani akan Hadisi nan na ‘ Umirtu an Ukatilan Nas…’
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
To, ya kai dan uwa ko ‘yar uwa mai girma wan Hadisin Annabin tsira Salallahu Alaihi wa Sallama ne, ba ayar Al-kur’ani ba ne. Hadisi ne ingantacce wanda malaman hadisi suke kira da MUTAWATIR. Manyan sahabbai kamar Abdullahi Ibn Umar, Abdullahi Ibn Mas’ud, Abu-Huraira, Anas Bin Malik, Abdullahi Ibn Amr da sauransu sun ruwaito hadisin daga Annabi SAW. Kuma har wa yau, gawurtattun marubuta hadisi sun ruwaito sa a cikin littafan su kamar Bukhari, Muslim, Abu-Dauwud, Turmuzi,
Nisa’i da sauransu.
Cikakken Hadisin An Ibn Umar radiyallahu anhu, anna rasulallahi salallahu alaihi wa sallama kala: Umirtu an ukatilan nasa hatta yash-hadu an la ilaha illallhu, wa anna Muhammadar Rasulul lahi, wa yukimus salata, wa yu’tuz zakata, fa iza fa’alu zalika asamu minni dima’ahum wa amwalahum illa bihakkil islami, wa hisabuhum alallahi ta’ala. (Bukhari da
Muslim)
Gundarin Fasarar Hadisin An karbo daga dan Umar, Allah ya yarda da su, Lallai Annabin Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya ce: “An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,
kuma Annabi Muhammadu manzon Allah ne, su tsaida Salla, su bada zakka,
idan suka yi haka sun tsare jininsu, da dukiyarsu, sai dai da wani hakki na musulunci, kuma hisabinsu na ga Allah madaukaki. (Bukhari da Muslim).
Ma’anar Hadisin An umurce ni da in yaki makiyan musulunci, wadanda suke yakinsa, kuma idan muka hadu a filin daga, kar in saurara musu, sai sun yi Imani da
Allah da manzonsa, sannan in saurara daga yakinsu. Kuma bayan imani in
tabbatar da cewa sun gina masallatai kuma sun tsaida Salla a cikinsu, kuma sun bada zakkar dakiyarsu tare da bin koyarwar addinin musulunci sau da kafa.
To, idan sun bi dokokin addini sau da kafa, sun tsare jininsu daga gare ni, ba zan yakesu ba, balle dukiyarsu ta zamo
ganima. Wato, jininsu da dukiyarsu sun haramta, sai dai wanda yayi wani abu da musulunci ya halatta jininsa ko dukiyarsa. Kuma hisabinsu na ga Allah masanin boye da bayyane.
Wannan hadisi baya nuna cewa musulmi su yaki duk wanda ba musulmi ba, musulunci yayi umurni da a kira wadanda ba musulmi ba zuwa ga musulunci da hikima, da kyakkyawan wa’azi, da kyautatawa tare da hujjoji masu karfi. Idan sunyi imani, to, alhamdu lillah, idan kuma ba suyi imani ba, to, babu tilas Lakum Dinikum Wa Liya Din.
Amma idan wasu suka ki imani, bayan wa’azi da ihisani, kuma suka kange
hanyar Allah, suka cutar da musulunci ko suka taimaka aka cuci addini, ko suka yaki musulunci, to an umurci musulmai da su kare kansu daga makiyan Allah, har sai sun dawo sunyi imani. Suratul mumtahina sura ta 60 aya ta 8-9 tana umurni ga musulmai da kyakkyawan mu’amala ga kafiran da basu yakesu ba. Kuma aya ta 13 a cikin Suratu Attauba sura ta 9 tana umuni ne da a yaki wanda ya fara yakin addini.
Allah shi ne mafi sani.
Allah ya zaunar da kasashen musulmi lafiya. Amin.