SUKUK: Majalisar Kolin Musulunci ta kwance wa Kungiyar Kiristoci zani a kasuwa

2

Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta ragargaji kungiyar Kiristoci ta CAN dangane da zargin da ta yi cewa tsarin tasarifin hada-hadar kudi na SUKUK, wata kullalliya ce domin a maida Nijeriya kasar Musulunci bai-daya.

SUKUK tsarin karbar kudi ne a karkashin addinin Musulunci, wanda ya samu karbuwa a cikin duniya, musamman a kasashen da ba Musulmi ba.

Jin cewa Gwamnatin Tarayya za ta rika bayar da kudin hada-hada a karkashin tsarin musulunci na SUKUK, sai CAN a farkon wannan satin ta fito ta kalubalanci tsarin.

Ganin haka, sai Majalisar Kolin Musulunci ta fito ta bayyana CAN da cewa zargin da take yi shirme me, gaulanci ne, kuma abin kunya ne.

Mataimakin Babban Sakataren kungiyar Salisu Shehu, ya ragargaji CAN, inda ya ce:

“Ta ya za a ce CAN ba ta da masaniyar cewa Bankin Duniya kan sa ya karbi tsarin SUKUK hannu bi-biyu.

” Abin sha’awa kuma shi ne kasashen da ba na musulmi duk sun karbi wannan tsari na SUKUK, saboda sun fahimci amfanin sa, ba cuta, ba cutarwa.

“A Afrika da Turai da yankin Asiya duk ana ta hada-hadar SUKUK. Kenya, Tanzaniya, Afrika ta Kudu, Ingila, Luxembourg, Rasha, China, Singapore da wasu kamfanin Amurka duk sun yi nisa da zurfi a cikin tsarin SUKUK.”

“Idan CAN ta manta, to bari na tuna musu cewa ko shekara biyu ba su cika ba, aka shirya wani gagarimin taro kan tsarin hada-hadar kudi na musulunci, wato SUKUK a London.

” A wurin, tsohon Firayi Ministan Ingila, David Cameron ya ce ai su aniyar kasar Ingila ita ce su yi wa tsarin kaka-gida, saboda tsari ne na yi wa juna adalci, kuma garabasa ce.

Shehu ya ci gaba da yi wa CAN tunatarwa cewa abin kunya ne su na su ma san cewa a nan Najeriya, jihar Kiristoci ta Kudu-maso-gabas ce ta fara garzayawa Bankin Musulunci na Islamic Development Bank, ta nemi lamunin kudi.

Daga nan sai ya yi wa CAN tsokacin cewa, abin da ake bukata a zamantakewa da juna shi ne yarda da juna, juriya da juna da kuma cin moriyar juna.

“Shin ko don mu ba mu da bakin magana ne shi ya sa ake cusa mana Kiristanci a kasar nan, amma ba ma cewa komai? An sa mana hutun dole a ranar Lahadi, amma mun kau-da-kai.

” Ga kuma alamar kuros a tambarin asibiti. Sunan Chancellor, Provost, Dean, Rector da sauran irin su a mukaman jami’o’in mu da manyan makarantu, duk Kiristanci ne fa.”

A karshe Shehu ya ce kawai shi bai san dalili ba da rana tsaka CAN ke kitsa tsoron addinin Musulunci su na cusa wa junan su.

Share.

game da Author