Gwamnonin Jihohin Kudu-maso-Gabas sun bayyana dalilan da ya sa su ka soke kungiyar tsagerun IPOB masu fafutikar kafa kasar Biafra.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin, Dave Omahi, Gwamnan Jihar Ebonyi ne ya bayyana dalilan yau Asabar, a fadar gwamnatin sa a garin Abakaliki.
Ya bayyana wa ‘yan jarida dalilai da suka hada da:
DALILAI 13 NA RUGUZA KUNGIYAR TSAGERUN BIAFRA
1. Saboda mu gaggauta dakatar da hargitsi da zaman dar-dar a yankin Kudu-maso-Gabas.
2. Saboda mun ga burkin tsagerun ya shanye, har sun wuce makadi da rawa, an fara kashe-kashe.
3. Saboda mun ga rikicin har ya shafi tattalin arzikin yankin Kudu-maso-Gabas.
4. Saboda tsagerun IPOB sun wuce gona da iri har sun tsokani sojoji, su na jifar su da duwatsu da kwalabe.
5. Mu na da shaidu cewa sojoji ba su kai wa tsagerun hari ba, su ne ma su ka rika jifar su.
6. Saboda idan wuta ta kama karamin abu, idan ba a kashe ta da gaggawa ba, sai ta cinye ko’ina gaba daya.
7. Wani algungumi mai suna Charles Ogbu ya yi ta tura lambar wayoyin gwamnonin kudu maso kudu da ta Shugaban Majalisar Dattawa da ma ta wasu manyan mutane. Aka rika kiran mu da tura mana yes, ana surface mana zagi na wulakanci.
8. Saboda tilas mu tashi mu kare rayukan ‘yan Arewa mazauna Kudu-maso -Gabas.
9. Saboda yawancin kabilar Ibo ba su goyon bayan kafa Biafra. Amma su na son a rika yi wa kowane yanki adalci.
10. Saboda yawancin tsagerun IPOB har da Nnamdi Kanu, ba wanda ya san illar yaki.
11. Saboda kowane yanki a kasar nan ya na da nasa korafin ha gwamnatin tarayya.
13. Saboda kuka ko korafin ana yi maka rashin adalci, ba dalili ba ne da za ka ce kai ala dole sai ka balle daga Najeriya.
13. Saboda babu wani gagararren da ya gagare mu mutstsikwa.