Shugaban hukumar kula da kawar da cututtuka na kasa NCDC Chikwe Ihekweazu yace gwamnatin tarayya za ta bada alluran rigakafin cutar shawara wa mutanen kasarnan.
Chikwe Ihekweazu ya ce gwamnatin tarayya ta amince da yin haka ne sanadiyyar bullowar cutar a jihohin Kwara da Kebbi.
Ya ce za a fara yin alluran rigakafin cutar daga ranar 30 ga watan Satumba.
Chikwe Ihekweazu ya yi kira ga mutanen jihohin da su dinga tsaftace muhallinsu, suna kuma kwana cikin gidajen sauro.
Ya shawarci mutane da su gaggauta kai duk wanda su ka ga ya kamu ko ya nuna alamun kamuwa da cutar kamar ciwon kai,zazzabi da sauran su sannan kuma su guji amfani da magunguna ba tare da izinin likita ba.