SERAP za ta zauna da Saraki domin sanin takamaiman albashin ‘yan majalisa

0

Wakilan kungiyar sa-ido kan bin ka’idojin aiki, SERAP, za ta zauna da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, domin tattauna yadda za a bayyana wa al’umma takamaiman albashin da ‘yan Majalisar Tarayya ke dauka.

“Mu na murnar sanar da cewa mun karbi takardar gayyata daga Shugaban Majalisar Dattawa, sakamakon wasikar da mu ka aika masa ta neman adadin kudin da ake bai wa ‘yan majalisar tarayya da na majalisar dattawa a matsayin albashi.”

Timothy Adewale, mataimakin daraktan SERAP, ya kara da cewa za mu yi amfani da wannan dama ta yin ido-da-ido da shugaban majalisar, inda za mu tambaye shi takamaimen yawan albashi da kuma alawus wanda kowannen su ke karba a duk wata.”

Adewale ya ce ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ya tuntubi SERAP ranar Talata, yayin da ya kuma yi nuni da cewa za a yi ganawar ne a ranar Alhamis.

Hakan dai ya biyo bayan wata wasika ce da SERAP ta aika wa Saraki, su ka nemi ya tabbatar musu shin naira milyan 29 ne albashin dan majalisar dattawa, kuma alawus din sun a shekara idan ya kai naira bilyan 3 a sherara.

Idan ba a manta ba, Shugaban Kwamitin baiwa shugaban kasa shawara akan batutuwan cin hanci da rashawa, Itse Sagay, ya ragargaji ‘yan majalisar dattawa har ya yi ikiranrin cewa wadancan adadin kudaden da aka bayyana a sama.

Share.

game da Author