Hukumar EFCC a jihar Gombe ta kama wani kwamishinan jihar Adamawa mai suna Sanda Lamurde, tsohon shugaban jami’iyyar PDP na jihar Abdurahman Bobboi da kuma wani Feredan da laifin wawushe kudaden kula da mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra a jihar.
Hukumar EFCC ta ce sun yi awon gaba da Naira miliyan 586 wanda gwamnatin jihar Adamawa ta ware musamman domin kula da mazauna sansanonin jihar.
Wanda ya shigar da karan Abubakar Aliyu ya roki alfarman kotun kada ta bada belinsu sannan ta tsayar da ranar sauraron karan.
Duk da cewa Sanda Lamurde, Abdurahman Bobboi da Feredan Geroge sun ki amincewa da zargin da aka yi musu alkalin kotun a jihar Bilkisu Aliyu ta yanke hukuncin kulle su a kurkuku har sai ta tabbatar da bada bellin na su.