Sarkin Katsina ya nemi Buhari ya amince da dokar kafa Dogarawan Tsaro

0

Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Usman, ya bayyana goyon bayan sa ga kudirin da aka zartas a majalisar tarayya domin amincewa da kafa dokar kafa Dogarawan Tsaro.

Kudirin dai zai amince da sauya Dogarawan Tsaro daga masu zaman kan su zuwa wani fannin jami’an tsaro na gwamnati.

Masu goyon bayan wannan tsari na kallon maida su karkashin gwamnati zai samar da kafar sama wa matasa masu dimbin yawa aikin yi.

Dalili kenan su ke cewa matsalar biyan su albashi ma kan sa ko an fa aiwatar da tsarin, to ba zai iya dorewa ba.

Haka nan kuma wannan kudiri ya na kan shan suka daga hukumomin tsaron Najeriya, musamman ganin cewa shugaban rundunar Dogarawan Tsaron, Dikson Akoh na a gaban alkali ana tuhumar sa da harkalla, dakasharama da kudade da kuma uwa-uba damfara.

Sai dai kuma baya ga mambobin majalisar tarayya da ke goyon bayan kudirin, shi ma ministan harkokin matasa da al’adu, Solomon Dalung ya na goyon bayan sa, kuma ya yi roko ga Shugaba Buhari da ya amince da kudirin.

Shi ma Mai Martaba Sarkin Katsina, ya bi sahun masu goyon bayan tsarin, kuma ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya amince da tsarin, ya na mai cewa dogarawan kiyaye zaman lafiya su na da matukar amfani kuma za su kara jaddada hanyoyin wanzar da zaman lafiya a cikin kasa.

Share.

game da Author