Sama da ‘yan Najeriya 10,000 ne ke karatu a Amurka

0

Sama da ‘Yan Najeriya 10,000 ne ke karatu a makarantu da jami’o’in kasar Amurka.

Wakilan kasar John Bray, ne ya sanar da haka da ya ke tallata makarantun kasar a wani taro a birnin Legas.

Bray ya ce sama da miliyan daya ne na dalibai daga kasashen waje ke shigowa kasar Amurka domin yin karatu duk shekara a makarantun kasar.

Ya Kara da cewa samun yawan daliban na nuna irin kusanta da dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Amurka ne.

Sannan Kuma ya ce kasar za ta ci gaba da ba ‘yan Najeriya fifiko waken samun gurabin Karo ilimi a kasar.

Share.

game da Author