Rundunar ‘yan sanda ta bada umurnin cire duk shingen binciken shige da Fice na ‘yan sanda a fadin kasarnan.
‘‘Za a cire duk shingen binciken da ke hanyoyin kasar musamman wadanda ke titunan Lagos-Ibadan, Shagamu-Benin, Benin-Onitsha, Okene-Abuja, Kaduna-Kano, Katsina – Kano, Otukpo – Enugu, Enugu – Port Harcourt domin samar wa matafiya da kayayaki saukin bin hanyoyin kasan’’.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Moshood Jimoh ya sanar da hakan a yau Talata inda ya kara da cewa rundunar na kira ga kowani dan sanda da ya yi biyayya da umurnin.
Moshood Jimoh yace rundunar ‘yan sandan ta amince akan hakan ne don ta wanke kanta daga zargin da ake mata akan cewa ma’aikatanta na amfani da shingen domin karban cin hanci sannan kuma da kawar da sace-sacen mutanen da ake yi a hanyoyin kasan
Don haka Moshood Jimoh yace rundunar ta kafa matakan tsaro wanda ake kira da ‘X squad’wanda ke da ikon cire duk shingen da aka kafa ba tare da izinin rundunar ‘yan sand aba sannan kuma za ta hukunta duk ‘yan sandan da ta kama.
Ya ce rundunar ‘yan sandan ta umurci duk ‘yansandan da suke aikin fataro a fadin kasan da su dunga sanya rigunan aikin su yadda ya kamata tare da sunayensu a jiki. Sannan su rubuta lambobin waya da mutane za su iya kira a duk lokacin da suke bukatan taimakon ‘yan sandan a jikin motocin.
Daga karshe rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga gwamanin jihohi da kananan hukumomin da su guji amfani da irin wannan shingen wajen karban haraji musamman yadda dokar kasan ta hana.
Discussion about this post