Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wasu matasa biyu da suka yi lalata da matan aure da karfin tsiya

0

Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kano ta kama wasu matasa biyu da suka aikata laifin lalata da wata matan aure da karfin tsiya.

Matasan masu suna Ali Shehu da Saifullahi Lawan mazauna unguwan Hotoro ne dake jihar Kano.

Kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta sanarwa manema labarai, sai da matasan suka shiga gidan suka aikata fashi sannan suka danne matan gidan karfi daya ji sukayi lalata da ita.

Kama wadannan barayi dai yasa an kamo wasu daga cikin abokan sana’arsu da suke zaune a wasu jihohin.

An kama Sabiu Umar a garin Rigachikum dake jihar Kaduna da wani Aliyu Shehu a jihar Nasarawa.

Bayan haka kuma an kwato Talabijin, komfuta, wayoyi da sauransu daga hannun barayin.

Daya daga cikin Barayin ya ce an kama shi ne a Unguwar Dorayi Babba da yake kokarin yi ma wani fashi.

Share.

game da Author